Gamayyar jam’iyyun adawa a ranar Talata, ta amince da jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a matsayin jam’iyyar siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.
Wannan dai wani babban mataki ne a yunkurinsu na ganin bayan jam’iyyar APC mai mulki.
Gamayyar ta kuma bayyana wasu daga cikin shugabannin riko da mambobin jam’iyyar.
Tuni dai aka nada tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, yayin da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, zai kasance sakataren kasa.
An nada tsohon ministan wasanni Bolaji Abdullahi a matsayin kakakin jam’iyyar.
Gamayyar dai ta yi kokarin yi wa wata sabuwar jam’iyya rijista, All Democratic Alliance, ADA, bayan tattaunawar farko da ADC da Social Democratic Party, SDP, ta wargaje.
Sai dai a lokacin da aka bayyana yunkurin na su na yin rajistar ADA na iya yin takaici daga hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, kungiyar ta koma tattaunawa da ADC.
An shirya gudanar da bikin kaddamarwar ne da karfe 2 na rana ranar Laraba.