Yayin da ake ƙasa da mako ɗaya gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Amurka, Kamla Harris ta shaida wa magoya bayanta a Washintong DC cewa, suna da zaɓi tsakanin ƴanci da hargitsi.
Da take jawabi a daidai wajen da Donald Trump ya shaidawa magoya bayaNsa cewa su yi zanga-zanga a shekarar 2021, Kamala ta bayyana abokin karawar na ta na jam’iyar Republican da wanda ba daidai yake ba, tana mai cewa ya ƙosa ya yi ramuwa.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen Harris dai ya ce wannan ne taro da mafi girma da ta taɓa yi, wanda mutane sama da dubu saba’in da biyar suka halarta.