Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum 288 da take da zargi da tayar da hankalin mutane a wajen zaɓen cike gurbin majalisar jihar da ake yi, inda ta ce ta ƙwato makamai da dama a hannunsu.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce Kwamishinan ƴansandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori ne ya jagoranci ƴansanda tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro da ke jihar wajen samun “nasarar dakile masu yunƙurin tayar da hargishin.”
“Mun fita ne domin ganin an gudanar da zaɓen cike gurbi a Ghari da Tsanyawa da Bagwai da Shanono lafiya.”
Ya ce sun samu nasarar kama mutum 288 da ake zargi ƴandaba ne masu yunƙurin tayar da zaune tsaye bisa laifuka daban-daban, sannan ya ce sun ƙwato makamai irin su adduna da bindigogin farauta da wuƙaƙe da gwafa da sauran su.
“Yanzu haka muna tsare da waɗanda muka kama, kuma da zarar mun kammala bincike, za a tabbatar an hukunta waɗanda aka tabbatar sun aikata laifi.”