A yammacin yau Talata ne ake sa ran mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, zai karbi bakuncin Sanatoci a jam’iyyar APC, domin buda azumin watan Ramadan.
A na dai kallon taron a matsayin wani bangare na tuntubar da ya ke yi da masu ruwa da tsaki a jam’iyya mai mulki kan neman takararsa na shugaban kasa a 2023.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata wasikar gayyata zuwa jam’iyyar APC a majalisar dattawa, mai dauke da sa hannun shugaban majalisar, Yahaya Abdullahi, kuma shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar ranar Litinin.