fidelitybank

Zaƙaƙurin tsohon ɗan wasan Manchester United Sir Bobby Charlton ya mutu

Date:

Tsohon zakakurin Manchester United, Sir Bobby Charlton, ya mutu yana da shekara 86.

Dan wasan ya taka rawar gani a gasar Kofin Duniya a 1966 da Ingila ta kartbi bakunci.

Charlton ya buga wa tawagar Ingila wasa 106 da cin kwallo 49 – ya dade a matsayin mafi bajinta a kasar kafin daga baya Rooney ya karba, sai kuma Harry Kane da ke rike da gurbin.

A shekara 17 da ya yi wa United tamaula, ya lashe kofin lik uku da European Cup da kuma FA Cup.

Iyalan Charlton sun sanar cewa ya mutu ne yana tsaka da bacci a kan gadonsa a sanyin safiyar Asabar.

A cikin watan Nuwambar 2020 aka bayar da sanarwar cewar Charlton ya kamu da cutar ciwon mantuwa.

United ta mika ta’aziyya ga iyalan Charlton da cewa “daya ne daga fitattun ‘yan wasan kungiyar da ya bayar da gudunmuwar da ba za a manta da shi ba”.

asuu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp