Kimanin mutum 22 ne suka mutu sakamakon fama da yunwa a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina.
Sansanin na dauke da dumbin ƴan gudun hijira da suke tsere daga garuruwan jihar da dama sakamakon karuwar matsalar tsaro a jihar.
Sansanin dai na dauke da akalla mutum 15,000 yawancin daga garuruwan Shimfida, da Zango, da Kwari, da Tsembe, da Tsauni da kuma Mai Wuya.
Rahotanni sun ce garuruwan sun zama tamkar kufai sakamakon hare-haren ƴan fashin daji.
Akwai yara akalla 3,000 a sansanin, baya ga mata da kuma tsofaffi, waɗanda da ƙyar da siɗin goshi suke samun abun kai wa ga bakin salati.
Malam Sa’ad Salisu Shimfida shi ne shugaban wannan sansanin ‘yan gudun hijira, ya kuma shaida wa BBC yadda waɗannan mutum 22 suka rasa rayukansu sakamakon fama da uƙubar yunwa.
Tun daga ranar 10 ga watan Maris da muka baro Shimfida da um kadai ne a sansanin, amma daga baya ƴan wasu garuruwan suka zo suka ƙru, hakan ya sa yawan mutane ya ƙaru amma abincin da muke samu bai ƙaru ba.
“Dalilin haka yara da dama da wasu mutanen suka mutu.
“Akwai ƙarancin abin shimfida, da yawa a ƙasa suke kwana, ga shi babu maganin sauro da na ƙwari duk babu.”
Dama dai a cewar shugaban sansanin tun kafin faruwar wanan al’amari, mutanen na rayuwa ne cikin kangin rashin abinci da ruwan sha, ga kuma kwana a kasa ba tare da abun shimfida ballantana na rufa ba.
Dangane da wanan batu BBC ta tuntubi shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Katsina, Alhaji Babangida Nasamu wanda ya musanta zargin.
“Ni da ma’aikatanmu na SEMA mun mayar da Jibiya kamar gida, kusan ko yaushe muna can kuma kullum muna magana da shugaban ƙaramar hukumar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a yanzu haka gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya ba da miliyan 100 don a tsugunar da ƴan gudun hijirar, kuma ana wadata su da abinci sosai.
Sai dai dama jihar Katsinan na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a arewacin kasar musamman ma satar jama’a, kuma akwai yan jihar da dama da ke gudun hijira a kwaryar birnin jihar, da kuma wasu jihohi makwabta.


