Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya bayyana cewa, fushi da yunwa da ake fama da su a fadin kasar nan ne ya sa aka shirya zanga-zangar.
Makinde ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a babban taron makon al’adu na Ibadan na shekarar 2024, wanda kungiyar ‘yan kabilar Ibadan ta tsakiya (CCII) ta shiryas.
An sanya ranar 1 ga watan Agusta a matsayin ranar gudanar da zanga-zangar adawa da yunwa a fadin kasar.
Makinde, yayin da yake jawabi ga mahalarta taron da aka gudanar a ranar Asabar a filin wasa na Obafemi Awolowo, Ibadan, babban birnin jihar, ya ci gaba da cewa mutane na da ‘yancin yin zanga-zanga.
Ya ce ‘yan Najeriya da ke shirin yin zanga-zangar nuna wahalhalun da ake fama da su a kasar, ya kamata su yi amfani da ‘yancinsu cikin lumana, kada su yi tashe-tashen hankula ko lalata kayayyakin jama’a.
Ya shawarci masu zanga-zangar da kada su lalata kadarorin gwamnati.
Makinde ya ce, “Najeriya na iya shiga cikin wannan hali a yanzu. Za mu iya fuskantar fushi da yunwa a cikin ƙasa don haka ne mutanenmu suke son yin zanga-zanga.
“Eh, zanga-zangar daidai ne. Amma ku tuna cewa mun yi amfani da kudinku ne wajen gina dukkan gine-gine da kayan aiki da muka sanya a jihar nan, ba nawa ba.
“Don haka, idan kuna son yin zanga-zangar, dole ne a kasance cikin lumana.
“Idan kun fara zanga-zangar ku, kada ku lalata kadarorin gwamnati, in ba haka ba, za mu yi amfani da kudaden da ya kamata mu kashe kan ayyuka masu ma’ana don maye gurbin wuraren da ka iya lalacewa.”