fidelitybank

Yunkurin EFCC a kotu na gurfanar da AA Zaura ya gamu da cikas

Date:

Yunkurin hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa, na gurfanar da ɗan takarar sanata na jam’iyyar APC a jihar Kano, AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura kan zarge-zargen tafka damfara ya sake fuskantar cikas a kotu.

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kanon ta ɗage gurfanar da A.A Zaura don bai wa sabon lauyansa dama ya je ya shirya don tunkarar shari’ar.

EFCC na zargin sa ne da damfarar wani ɗan ƙasar Kuwait kuɗi fiye da dala miliyan daya, zargin da ya sha musantawa.

Karanta Wannan: EFCC ta kama mutane 6 masu damfara ta Internet

Duk da kasancewar EFCC ta sami nasarar kawo AA Zaura gaban kotun tarayyar amma kotun ta ɗage zaman shari’ar saboda sabon sauyansa Basil Hemba bai shirya ba, inda yace yana buƙatar nazarin yadda zai tunkari batun kasancewarsa sabo kan shari’ar. iN J

Lauyar EFCC Bar. Aisha Habib ta nemi kotu ta ci gaba da sauraron shari’ar saboda ta ce sun shirya kuma sun kawo wanda ake zargin kotu, sai dai sabon lauyan AA Zaura ya ce bai shirya ba kasancewar jiya ya karɓi kunshin Shari’ar.

Wannan shi ne karo na shida da ake ƙoƙarin gurfanar da AA Zaura, amma har yanzu ba a kai ga karanto masa zarge-zargen da EFCC ke masa a gaban babbar kotun tarayyar ba.

Saboda a cewar Lauyar EFCC Bar. Aisha Habib ana ta gabatar da uzuri iri daban-daban.

Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa ya ɗage zaman kotun zuwa 1 ga watan Maris, don bai wa sabon lauyan damar nazartar ƙunshin Shari’ar.

Bayanai na cewa wata babbar kotun tarayya a 2020 ta sallami AA Zaura tare da wanke shi kan da duk wani zargi da EFCC ke masa, abin da yasa EFCCn sake gabatar da zargin zamba da ake yi masa tun da farko a kotu.

the nation newspaper nigeria today latest

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp