Kamfanin Youtube ya goge tashar da ke wallafa bidiyon marigayi Fasto TB Joshua saboda saba ka’idojin furta kalaman kiyayya.
Matakin ya zo makonni bayan wani bincike da BBC ta gudanar inda kungiyar Open Democracy ta bankaÉ—o shaidun cin zarafin mata da azabtarwar da marigayin ya yi a lokacin da yake raye.
Tashar Emmanuel TV ta taka rawa sosai wajen É—aga faston da ya zama fitacce a duniya.
A shekarar 2021 ne TB Joshua ya mutu sai dai cocinsa na Synagogue ya ci gaba da tafiyar da harkokinsa a karkashin mai É—akinsa Evelyn Joshua.
Har yanzu cocin bai ce komai ba kan cire tashar daga Youtube sai dai ya ƙaryata zarge-zargen da aka yi wa marigayin.
Tashar ta Emmanuel TV tana da mabiya fiye da rabin miliyan a kafar ta Youtube sannan miliyoyin mutane ne ke kallon bidiyon da tashar ke wallafawa.
Wannan ne karo na biyu cikin shekara uku da Youtube ya dakatar da tashar saboda take wasu dokokin tafiyar da tasha a Youtube.
A wani bangare na binciken da BBC, OpenDemocracy ta yi nazari kan bidiyon da tashar Emmanuel TV take wallafawa inda ta gano akwai bidiyo akalla 50 na cin zarafi a Youtube.
Tawagar kungiyar sun shigar da korafinsu kan bidiyon ga Youtube inda aka dakatar da tashar a ranar 29 ga watan Janairu.