A ranar Litinin ne Majalisar Dokokin Jihar Yobe, ta zabi Hon. Chiroma Buba Mashio a matsayin shugaban majalisa ta 8.
Ana sa ran Mashio zai jagoranci harkokin Majalisar a cikin shekaru hudu masu zuwa.
Sabon shugaban majalisar dai shi ne dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress a kan mukamin bayan da shugabannin jam’iyyar APC suka yanke shawarar bai daya a jihar a jiya.
A cewar jam’iyyar, sauran manyan jami’an da za su yi aiki a majalisar ta 8 a jihar su ne Hon. Hussaini Mohammed Yusufari (Mataimakin shugaba), Hon. Muhammed Auwal Isa Bello (Cif Whip), Hon. Ahmed Musa Musa Danbol (Mataimakin Cif-Hip), Hon. Nasiru Hassan Yusuf (Jagora) da Hon. Yau Usman Dachia (Mataimakin Kakakin Majalisa).
Mashio shine dan majalisa mafi dadewa a majalisar, daga 1999-2023.


