fidelitybank

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Date:

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta ce mamakon ruwan sama da yin gine-gine kan magunan ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri.

A ranar Laraba ne aka samu rahotonni ambaliya a wasu unguwannin birnin Maiduguri da yankin ƙaramar hukumar Jere sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka shafe tsawo sa’a uku a tafkawa a birnin.

Cikin wata sanarwa da shugaban hukumar NEMA, Zubaida Umar ta wallafa a shafinta na Facebook ta danganta ambaliyar da rashin bin tsarin gine-gine.

”Ambaliyar na da alaƙa da mamakon ruwan sama da aka samu a birnin da kuma rashin kula da kwalbatoci da yin gine-gine kan hanyoyin da ruwa ke bi”, in ji shugabar ta NEMA.

Hukumar ta NEMA ta ce jami’anta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi sun taimaka wajen ceto mutanen da ambaliyar ta rutsa da su tare da rage illar ambaliyar.

Ambaliyar na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan wata mummunar ambaliyar da ta auka wa yankin, wadda ta yi sanadiyyar raba fiye da mutum miliyan guda da muhallansu.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp