Mawakiyar Najeriya, Yemi Alade, za ta baje kolin wakar ta a bikin bude gasar cin kofin Afrika na 2023, AFCON.
A ranar Asabar 13 ga watan Junairu, 2024 ne aka shirya bikin bude gasar ta AFCON.
Da take sanar da wannan labari a wani sako da ta wallafa a shafinta na X, mawakiyar ta bayyana ci gaban a matsayin mafarkin gaskiya ta tabbata.
“Ba zan iya mantawa da mahimmancin addu’a da faÉ—in abin da zuciyarku ke so ba.
“Tun daga shekarar 2016, ina sha’awar yin wasa a filin wasa don bukukuwan kwallon kafa da ke kewaye da daruruwan ’yan rawa da mutane.
“Bayan shekaru 7, ina taka leda a AFCON. Lallai abin alfahari ne kuma mafarki ne ya tabbata. Mafari ne kawai.”