Mataimakin kakakin majalisar wakilai Rt. Hon. Ahmed Idris Wase, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da magoya bayan jam’iyyar APC cewa, an samar da dukkanin tsare-tsare na tsaro, domin tabbatar da tsaron dukkan jiga-jigan da za su halarci gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Talata.
A cewar kwamitin shirya taron na yankin, jam’iyyar APC a jihar Filato kuma a shirye take ta karbi bakuncin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a Jos, kasancewar Filato gidan APC ne.
Hon Idris Maje Wase wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma’a a Jos, ya yabawa jam’iyyar APC bisa zabar Filato da ta yi a yakin neman zabe.