Ma’aikatar Kuɗi ta China ta sanar da kashi 84 cikin 100 a matsayin ƙarin haraji kan kayan Amurka da ake shigarwa ƙasar.
Ma’aikatar ta ce ƙarin zai fara aiki daga ƙarfe 5:00 na asubahin Alhamis agogon Najeriya.
Ƙasashen duniya dai na ta ƙoƙarin tunkarar yadda za su ɗauki fansa.