Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce yaƙin da ake yi tsakanin Isra’ila da Gaza ya ”ɗauke hankali duniya” daga yaƙin da ake yi a ƙasarsa.
Ya ce wannan na ”ɗaya daga cikin burin” Rasha, wadda ta ƙaddamar da mamaya kan Ukraine a watan Fabrairun 2022.
Mista Zelensky ya musanta batun cewa yaƙin Ukraine ya ƙi ci ya ki cinyewa, duk kuwa da iƙirarin hakan da babbar hafsan sojin ƙasar ya yi.
Yayin da yake jawabi ga shugabar hukumar tarayyara Turai, Ursula von der Leyen da ta ziyarci birnin Kyiv, mista zelensky ya ce ”A bayyane take yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ya ɗauke hankalin duniya” daga na Ukraine.