Tsohon shugaban shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gargaɗin cewa yadda al’ummar ƙasa ke ƙaruwa cikin sauri ka iya zama matsala ga ƙasar nan matukar ba a ɗauki matakan da suka dace ba.
Yayin da yake jawabi wa manema labarai a Daura jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi, tsohon shugaban ƙasar ya ce yawan ƙaruwar jama’a a ƙasar abin dubawa ne.
”Yadda al’umma ke ƙaruwa cikin sauri matuƙar ba a ɗauki mataki ba, zai kawo matsala ga al’umomi masu tasowa”.
“Don haka akwai buƙatar gangamin wayar da kan al’umma kan wannan matsala, tare da buƙatar zuba jari a ɓangarorin ilimi da na lafiya.”