fidelitybank

Yawan yaran da ke fama da karancin abinci mai gina jiki na karuwa a Borno

Date:

Mazauna jihar Borno dama jami’na lafiya sun bayyana damuwa a game da karuwar yaran da basa samun abinci mai gina jiki sakamakon yunwa da iyayen da ke shayar da yaran ke fama da ita.

Rahotanni sun ce yawancin mutane da ke zaune a kananan hukumomin arewacin jihar kamar Marte da Kukawa da Abadam da Guzamala da Kaga da Mobbar da kuma Gubio sun dogara ne da kayan agajin da ake kai musu.

Da suke Magana da jaridar Daily Trust, mazauna wadannan yankuna sun bayyana matukar damuwarsu a kan tsananin yunwar da ake fama da ita sakamakon barazanar da Boko Haram ke yi musu a yankunan.

Wani mai gida da jaridar ta tattauna da shi ya ce, rashin abincin da iyaye masu shayarwa za su ci ne ke sa yaran da ake shayarwa basa samun abincin da zai gina musu jiki.

Ya ce sai iyaye mata masu shayarwa sun ci sun koshi kafin su samu ruwan nonon da zasu shayar da’ya’yansu.

Ya kara da cewa,ā€ Barazanar ā€˜yan Boko Haram ta tilasta mana barin ainihin muhallanmu, abin da ya sa a yanzu kullum sai mun fita domin neman abin da zamu kai wa iyalanmu su ci, ba za mu iya komawa garuruwanmu na asali ba saboda tsira da ranmu.ā€

A yanzu asibitoci na cika da yaran da ke fama da karancin abinci mai gina jiki.

Duk da kokarin da kungiyar likitoci ta Medicins San Frontiers ke yi da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya wajen shawo kan wannan matsala, tallafin da ake bayarwa bai wadatarba.

Shugaban kungiyar tabbatar da adalci ta jihar Borno BOSAM, Ahmed Shehu, ya bukaci gwamnati da ta mayar da hankali wajen kirkirar abubuwan da za su rinka kare lafiya da walwalar yara a jihar. In ji BBC.

dailypostnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuʙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miʙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin Ę“an Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaʙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

ʊan takarar shugaban ʙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ʙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alʙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp