Babban Bankin Duniya, ya yi hasashen cewa, yawan talakawa a Najeriya zai ƙaru zuwa mutum miliyan 95 a bana.
Ya bayyana haka ne a cikin wani rahotonsa mai taken “ƙoƙarin samarwa ‘yan Nijeriya makoma ta gari.”
Ya ce, rage radadin fatara ya fuskanci cikas tun shekarar 2015 inda ‘yan Najeriya da dama suka fada cikin kangin talauci a tsawon shekaru.
A cewar Bankin an yi hasashen adadin talakawan da za su fada cikin kuncin rayuwa a Najeriya zai kai miliyan casa’in da biyar da dubu dari daya a shekarar 2022.