Shugabannin ƙasashen yankin Afrika ECOWAS, na gudanr da taron, Afrika na kwana biyu a Habasha inda ake sa ran batun juyin mulkin da aka yi a ƴan kwanakin nan wasu ƙasashen Afrika zai zama babban abin tattaunawa.
An dai dakatar da ƙasashen nahiyar Afrika guda huɗu daga zuwa wurin taron a bara sakamakon sauyin da aka samu a ƙasashen a tsarin mulkinsu, kuma ƙasa ta baya-bayan nan da aka haramta wa zuwa taron ita ce Burkina Faso.
Ana sa ran shugabannin za kuma su tattauna kan batun annobar korona da kuma batun sauyin yanayi.
Ana gudanar da taron ne a Addis Ababa, birnin da a yan kwanakin nan ƴan tawayen Tigray suka yi barazanar shiga a yaƙin da suke yi da sojojin tarayyar Habasha.