fidelitybank

Yau wanda yake talla a titi ne ya taso ya zama Sarki – Osimhen

Date:

Ana jinjina wa “sabon sarki a Afirka,” Victor Osimhen bayan an bayyana sunan ɗan wasan gaban na Najeriya, a matsayin Gwarzon Ɗan ƙwallon nahiyar na Shekara ta 2023.

Ɗan ƙwallon na kulob ɗin Napoli mai shekara 24, ya karɓi wannan lambar yabo ne a daren Litinin, yayin bikin ba da lambobin karramawa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Aifrka (Caf), inda ya murƙushe hamayyar abokan karawarsa kamar kyaftin ɗin Masar Mohamed Salah da ɗan bayan Moroko Achraf Hakimi.

Ga Osimhen, wanda ya taso a titunan turɓaya na unguwar Olusosun cikin birnin Lagos, wannan wani “cikar burin rayuwa” ne bayan ya fuskanci tsananin gargada a lokacin yarintarsa.

“Ina miƙa godiyata ga kowa da kowa da ya taimaka mini a wannan tafiya, da kuma duk ‘yan Afirka da suka taimaka wajen ɗora ni kan wannan matsayi duk da matsalolina,” cewar Osimhen.

Osimhen wanda a kullum ɗoyin tarin bola yake yi masa sallama a unguwarsu, ya ce yana da maitar burin cimma nasara, duk da ƙalubalen da ya fuskanta a rayuwa.

Sai da ya yi tallan jarida, kuma ya yi sana’ar sayar da ruwan roba, lamarin da ya bayyana da kasancewa a halin “rayuwa mafi wahala”.

“A matsayina na yaron da ya taso yana talla a tsakanin motoci a kan titi kusan a kullum, don kuɓuta daga ɗumbin ƙalubalen da ni da iyayena muka yi fama da shi, zamowa mai irin wannan daraja a Afirka da ma duniyar ƙwallon ƙafa, wani katafaren buri ne a gare ni,” ya rubuta cikin wani saƙo a dandalin X.

“Gwagwarmayar ƙwallon ƙafata, ta kasance wani lilo mai hawa da gangara cike da gargada da kuma shauƙi.”

“Cikar buri da murnar nasarori ne suka riƙa yi min ƙaimi, hatta a lokacin da masu suka da nuna ƙiyayya da zafin kaye suka riƙa bugun ƙirjina da ƙarfi.”

Bayan ya ci ƙwallo 26 ne ya taimaka wa Napoli ta lashe gasar Serie A ta farko a cikin shekara 33, Osimhen ya zama ɗan Najeriya na ɗaya da ya ci lambar karramawa ta Caf a ɓangaren maza tun bayan tsohon ɗan wasan gaban Arsenal, Nwankwo Kanu a 1999.

“Abin da Osimhen ya yi ya fi ƙarfin hankali,” in ji tsohon ɗan ƙwallon Arsenal daga ƙasar Togo Emmanuel Adebayor, wanda ya lashe irin wannan lambar yabo ta Afirka a 2008.

“Cin ƙwallaye mai yiwuwa abu ne mai sauƙi a Ingila amma yin haka a Italiya ba mai sauƙi ba ne saboda suna ƙarfi a wajen tsare baya da kuma tsara dabarun wasa.”

Yayin da shi kansa tsohon ɗan wasan gaban Ivory Coast Didier Drogba, wanda sau biyu yana ɗaukar lambar lambar Caf ta Gwarzon Afirka na Shekara, ya bayyana tsohon ɗan wasan gaban Lille a matsayin sabon sarkin ƙwallon ƙafan Afirka, kuma yanzu akwai kyakkyawan fatan cewa zai ingiza Najeriya zuwa ga wani sabon zangon nasara.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp