A yau Talata ne, al’ummar Jamhuriyar Nijar suka gudanar da idin karamar sallah, abin da ya kawo karshen watan azumin Ramadan na bana.
A filin idi da ke Zone Industrielle a Yamai, babban birni ƙasr, mutane ne suka cika domin yin sallar.
Bikin sallah a ƙasar na zuwa ne bayan da hukumomi suka sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a faɗin jihohi biyar na ƙasar.