Ranar Lahadi za a kammala Premier League, wadda za a yi karawa 10 a kuma lokaci ɗaya, kenan fafatawar mako na 38.
An fara gasar ranar 16 ga watan Agustan 2024, kuma kawo yanzu an buga karawa 370 da cin ƙwallo 1,091, inda ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah shi ne kan gaba a cin ƙwallaye mai 28 a raga.
Tuni Liverpool ta lashe kofin bana na 20 jimilla, irin yawan na Manchester United.
An kuma samu ukun da suka yi ban kwana da Premier da ya haɗa da Leicester City da Ipswich Town da Southampton.
Yanzu abin da ya rage shi ne waɗanda za su wakilci Ingila a Champions League da Europa da Conference League.
Liverpool da Arsenal sun samu gurbin Champions League har da Tottenham, wadda ta lashe Europa League.
Yanzu saura gurbi uku ake nema a teburin Premier da za su je babbar gasar zakarun Turai.