fidelitybank

Yau ake sa ran shugaban NLC zai bayyana a ofishin ƴan sanda bisa tuhumar sa da ta’addanci

Date:

Hukumar ƴansanda  ta gayyaci shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa, Joe Ajaero da ya bayyana gabanta domin amsa tambayoyi waɗanda ke alaƙa da zargin tallafa wa ta’addanci da take yi masa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin mataimakin kwamishinan ƴansanda ɓangaren jami’an tattara bayanan sirri.

Sanarwar da ta samu saka hannun Adamu Muazu, jami’in yaɗa labaru na hukumar, ta ce tana kuma zargin shugaban na NLC da kutse a intanet da kuma sauran abubuwa.

Hukumar ƴansandan ta yi barazanar cewa muddin bai amsa goron gayyata da ta yi masa ba, hakan zai janyo ta kama shi.

“Ofisihinmu na binciken Ajaero kan zargin haɗa baki don aikata zamba, tallafa wa ta’addanci, cin amanar ƙasa da kuma kutse a intanet,” in ji sanarwar da ƴansandan suka fitar.

Sanarwar ƴansandan ta ƙara da cewa ana son shugaban na NLC ya bayyana ne a Talata 20 ga watan Agusta da misalin karfe 10 na safe domin amsa tambayoyi.

nigerian 
newspapers today the sun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...
X whatsapp