Yaron nan ɗan ƙasar Morocco mai suna Rayan ɗan shekara biyar wanda ya faɗa cikin rijiya ya rasu, duk da ƙoƙarin da aka yi ta yi na ceto shi.
Masarautar ƙasar ce ta sanar da rasuwarsa jim kaɗan bayan ciro shi daga rijiyar.
Jam’a da dama ne suka taru tsawon kwanaki a wurin da lamarin ya faru, domin jira su ga an ceto yaron, haka kuma an ta tattauna wannan batu a shafukan sada zumunta inda aka yi ta buƙatar gwamnatin ƙasar da ta yi ƙoƙarin ceto shi.
Yaron ya faɗa ne cikin rijiyar mai tsawon mita 32 tun a ranar Talata. Sai dai tsoron zaftarewar ƙasa na daga cikin abubuwan da suka kawo cikas wajen aikin ceton nasa.
Yan kallo sun yi ta murna da shewa lokacin da ma’aikatan agajin gaggawa suka ceto yaron, bisa tunanin ya rayu, sai dai daga baya murna ta koma ciki.