Mahalatta taron majalisar dinkin Duniya na sauyin yanayi da ke gudana a Masar, sun yi gargadin cewa yarjejeniyar da ake yi na tafiyar hawainiya fiye da yadda aka yi tsammani.
An tsara kammala taron kolin ne a gobe Juma’a, amma har yanzu akwai rarrabuwar kai sosai a kan wasu muhimman batutuwa.
Kuma dole ne a shawo kansu kafin a cimma wata matsaya.
Wani abu da ya zama alakakai shi ne, batun bayar da kudade ga kasashe mafiya rauni da ke ganin illar sauyin yanayin muraran, kan nawa za a biya su, da kuma waye zai biya.
Wani batun kuma shi ne shawarar da Indiya ta gabatar ta kowa ya kuduri aniyar kawar da amfani da duk wani makamashi mai gurbata muhalli, maimakon a ce kwal kawai.