Yariman Wales mai jiran gadon sarautar Birtaniya, ya buɗe taron shugabannin kasashen Commonwealth a Kigali babban birnin kasar Rwanda.
Ya ce, kowace ƙasa za ta iya yin nata tsarin mulki, yana mai cewa, abubuwan na iya sauyawa cikin natsuwa ba tare da tada jijiyoyin wuya ba.
Yarima Charles ya kuma tabo batun cinikin bayi, yana mai cewa yana so ya amince da kuskuren da aka aikata a baya.
Ya ce, ba zai iya misalta girman bakin cikinsa na kuncin da mutane da dama suka shiga ba a lokacin.
Shugabanni da dama daga kasashen da Burtaniya ta rena ne ke halartar taron, ciki hadda Shugaban Muhammadu Buhari.