Sanata Abdulaziz Yari ne ya yi tambayar farko, inda ya nemi sanin abin da El-Rufai zai yi don inganta samar da lantarki a Najeriya idan majalisar ta tabbatar da shi, kuma shugaba Tinubu ya naɗa shi ministan lantarki.
Sanata Karimi Sunday daga Kogi ta yamma ya ja hankalin majalisar a kan abin da ya kira ”Ƙorafi mai ƙarfi kan El-Rufai amma majalisar ba ta saurare shi ba.
Daga nan sai Sanata Khalid Ibrahim Mustapha mai wakiltar Kaduna ta Arewa ya nemi majalisar ta bari El-Rufai ya yi gaisuwa ya wuce, inda ya kafa hujja da matsayar da majalisar ta cimma a baya kan mutanen da suka taɓa zama minista ko gwamna.
Majlisar ta amince da buƙatar sanata Khalid amma ta buƙacin El-Rufai ya amsa tambayar da sanata Yari ya yi masa.
Da yake bayar da amsa, El-Rufai ya ce Najeriya tana da ƙarfin samar da lantarki ta kuma rarraba ta ga jama’ar ƙasar.
Ya ce dole a samar da sabbin kamfanonin rarraba lantarki a Najeriya don kuwa daga cikin kamfanoni 11 dake wannan aiki a yanzu uku ne kacal ke tafiyar da aikin su yadda ya kamata.
Tsohon gwamnan jihar Kadunan ya ce aikin gyara ɓangaren lantarki a Najeriya abu ne mai buƙatar haɗin gwiwar kowanne ɓangare.