Babban Sufeton Ƴansan kasar nan, Kayode Egbetokun ya ce, waɗanda suka suma a kotu su shida cikin waɗanda aka kai kan zargin zanga-zangar tsadar rayuwa sun yi hakan ne da gangan domin ɗaukar hankali da ɓata sunan hukumomi.
An gabatar da masu zanga-zangar ne su 114, jiya, Juma’a a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda kafin gurfanar da su, huɗu daga cikinsu da suka hada da yara biyu suka faɗi, inda aka garzaya asibiti da su.
Lamarin ya ɗauki hankalin duniya tare da janyo maganganu a cikin ƙasar, inda da dama ke suka a kai.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan Muyiwa Adejobi ya fitar a madadin Sufet Janar ɗin, kakakin ya jadda cewa a ƙarƙashin dokokin Najeriya duk mutumin da ya kai shekarun munzalin aikta laifi, to alhakin wannan laifi da ya yi ya rataya a wuyansa ko yaya shekarunsa suke.
Sanarwar ta ce laifukan da ake tuhumar mutanen da aikatawa sun haɗa da lalata kayan gwamnati da barazana ga tsaron ƙasa da sauransu.
Alƙalin kotun ya bayar da belon kowannensu a kan naira miliyan goma da kuma mutum biyu masu tsaya wa kowanne.