fidelitybank

Yara miliyan 61 sun rabauta da allurar rigakafi a Najeriya

Date:

Gwamnatin Tarayya ta ce, kimanin ƴan ƙasa miliyan 61 da dubu ɗari biyar ne aka yi wa rigakafin cutar maleriya, ƙyanda, shawara, ƙyandar biri da kwayar cutar HPV mai janyo sankarar bakin mahaifa.

Hukumomi a ƙasar sun ce mafiya yawa daga cikin waɗanda aka yi wa rigakafin yara ne ƙanana.

Kuma alkaluman an tattara su ne tun daga shekarar 2023 zuwa yanzu.

Shugaban hukumar kiwon lafiya a mataki na farko na ƙasar, Muyi Aina, ya sanar da hakan a wani taron bikin makon rigakafi na Afrika da aka yi a ranar Talata a Abuja.

Inda ya ƙara da cewa aƙalla yara kusan miliyan 26 ne da ke zaune a jihohu 26 na ƙasar aka yi wa rigakafin ƙyanda a shekarar 2024.

Yayin da wasu miliyan 22 da dubu ɗari biyar da ke jihohin Borno, Yobe da kuma jihar Legas suka ƙarbi rigakafin shawara.

A ƙasar ta Najeriya ana samun ɓullar wasu cututtuka da suke shafar yara daga lokaci zuwa lokaci, waɗanda kuma a wasu lokutan kan kai ga asarar rayuka.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp