Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce, aƙalla yara miliyan 242 ne suka samu akasi a harkokin karatunsu, a shekarar da ta gabata saboda matsaloli masu alaƙa da sauyin yanayi.
Tsananin zafi da guguwa da ambaliya sun shafi makarantu a ƙasashe tamanin da biyar na duniya, inda nahiyar Asiya ta fi fuskantar wannan matsala.
Asusun ya ce yara ne suka fi cutuwa sakamakon tsananin zafi fiye da manya, kuma taɓarɓarewar harkokin ilimi na iya sa su su daina zuwa makaranta musamman ƴaƴa mata.
Asusun ya ce yana bayar da taimako don sake gina makarantu da waɗannan matsaloli suka shafa, tare da inganta ilimi game da sauyin yanayi don ƙarfafawa yara su zama abin da ta kira wakilan sauyi.