Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi gargadin cewa akalla yara miliyan 1.6 ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa maso Gabas.
Shugaban ofishin UNICEF na Maiduguri Phuong Nguyen ne ta bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na gidauniyar a Arewa maso Gabashin Najeriya, wanda aka gudanar a Maiduguri ranar Laraba.
Ta nanata cewa UNICEF ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta bar wani yaro a baya yayin da take kokarin inganta harkar ilimi a Najeriya.
Ta kuma jaddada bukatar gwamnati, UNICEF, kungiyoyin bayar da agaji da sauran abokan huldar ci gaba su raba sabbin hanyoyin da aka koya daga aiwatar da shirye-shirye daban-daban a yankin.
“Aƙalla yara miliyan 1.6 ba sa zuwa makaranta a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.
“A cikin waÉ—anda ke makaranta, kashi 72 cikin 100 ba za su iya karanta rubutu mai sauÆ™i ba bayan aji na 6. Ba tare da samun ingantaccen tushe da Æ™warewa ba, yara sun kasa ci gaba a makaranta da rayuwa.