Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa yara mata miliyan 7.6 a Najeriya, mafiya yawa daga yankunan arewacin kasar, ba sa samun damar karatu.
Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Cristian Munduate ce ta bayyana hakan a gidan gwamnatin Kano yayin bikin tunawa da ranar yara mata ta duniya ta shekarar 2023 da aka yi wa taken: “Lokacinmu ne yanzu hakkinmu, makomarmu.”
Ta ce, “Yayin da nasarorin da ‘yan mata ke samu ke bayar da kwarin gwiwa ga sauran mata a wasu sassan duniya, yara mata miliyan 7.6 a Nijeriya, mafi yawa daga yankunan arewa ba sa samun wannan dama ta karatu.”
“Abin ban tsoro shi ne, Najeriya na da kashi 15 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta a duk duniya. Amma duk da haka, kashi 9 cikin 100 na matalautan mata ne ke da damar zuwa makarantar sakandare. Wannan ba ƙididdiga ba ce kawai, kira ne na a tashi tsaye.”
“Amma ko yaya, a cikin waɗannan ƙalubalen, muna samun karin kwarin gwiwa a yau da gobe.”
Ta kara da cewa, a yayin da Kano ke matsayi na biyu a jerin ‘yan matan da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, lamarin da ya nuna akwai tsananin banbance-banbance wajen samun ilimi, akwai bukatar a kara jaddada canjin wajen samar da ilimi.