fidelitybank

‘Yar uwar Jonathan ta mutu ta na da shekaru 70

Date:

Yar uwar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Madam Obebhatein Jonathan ta rasu.

Obebhatein ya rasu yana da shekaru 70 bayan gajeriyar jinya a ranar Alhamis a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Yenagoa a jihar Bayelsa.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Jonathan, Ikechukwu Eze ya fitar.

Sanarwar ta ce marigayiyar wadda aka fi sani da Amissi, malama ce mai ritaya, ‘yar kasuwa, uwa mai kauna kuma kakarta wacce ta sadaukar da rayuwarta ta bautar Allah da kuma bil’adama.

Ya kara da cewa ita kirista ce mai kishin kasa, mace tagari kuma abin koyi ga mutane da yawa a ciki da wajen al’ummarta.

Sanarwar ta kuma nuna cewa an shirya binne gawar ranar Talata 16 ga watan Fabrairun 2024, inda ta jaddada cewa iyalan za su sanar da cikakkun bayanai game da jana’izar.

Madam Obebhatein Jonathan ta bar ‘ya’ya uku, ‘yan’uwa, ciki har da mai girma Dokta Goodluck Ebele Jonathan, da mahaifiyarta, Mama Eunice Afeni-Jonathan.

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp