A ranar Juma’a n,Owowoh Princess Oluchukwu, ta zama mace ta farko ƴar Najeriya da ta kammala karatu a Kwalejin sojoji ta Sandhurst da ke Birtaniya.
Oluchukwu mai shekaru 24, ta kasance ɗaya daga cikin jami’an Cadets 135 da suka kammala karatu yayin wani fareti da aka shirya a birnin Landan a ranar ta Juma’a.
A shekarar 2018, Princess ta shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA), a jihar Kaduna.