Wata ƴar Najeriya ta ce ta shafa wa farata fiye da dubu huɗu jan-farce cikin sa’a 72 a yunƙurinta na shiga kundin bajinta na duniya.
Lisha Dachor mai shekara 19 ta yi ta kara-kaina a wurin taron a jihar Filato da ke arewacin Najeriya inda ta riƙa shafa wa mata jan-farce mai launin kaloli.
A ranar Laraba ne, matashiyar ta kammala shafe kwana uku tana sa wa mutane jan-farcen.
Kundin bajinta na Guinness ya ce idan har Ms Dackor na son ta kafa tarihi dole ne ta shafa jan-farce kan farata 60 cikin sa’a ɗaya.
A yanzu tana dakon Guiness ya yi nazari kan bidiyon da za ta tura masu.
Ms Dachor ta ce ta yanke shawarar ta yi haka ne domin kawo sauyi ga rayuwar mata da ke rayuwa da yara ba tare da mazaje ba.
“Ina son na bai wa mutane ƙwarin gwiwa musamman iyaye mata da ke kula da yaransu saboda mutane da dama suna tunanin ba su da wani abin nunawa,” kamar yadda ta shaida wa BBC.
Matashiyar wadda ƙwararriya ce a fagen sa ka jan-farce, ta shafe kusan shekara uku inda ta ce tana son fito da mata ƴan arewacin Najeriya a idn duniya.
Ms Dachor ta kuma yi fatan yunƙurin nata zai haskaka Filato, jiharta ta asali.