Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika CAF, ta nada Dorsaf Ganouati ‘yar kasar Tunisia a matsayin alkalin wasa na tsakiya a karawar da za a yi tsakanin Banyana Banyana ta Afrika ta Kudu da Super Falcons ta Najeriya.
Za a buga wasan karshe na neman tikitin shiga gasar Olympics na 2024 a filin wasa na Lotfus Versfeld, Pretoria, ranar Laraba.
‘Yan uwan Ganouati, Houda Afine da Emna Ajbouni, za su kasance mataimaki na farko da jami’ai na hudu bi da bi.
Yara Atef Saïd Abdelfattah daga Masar ne zai zama mataimakin alkalin wasa na biyu.
Agar Mezing ta Kamaru ce za ta zama mai tantance alkalin wasa, yayin da Cindy Dludlu daga Eswatini za ta zama kwamishinan wasa.
Super Falcons ta samu nasara a karawar farko da ci 1-0 a bugun fenariti da Rasheedat Ajibade ta samu.