Kundin tarihi na Guinness ya yi watsi da yunƙuri da wata ƴarƙasar Ghana ta yi na kafa wani sabon tarihi na wadda ta ɗauki lokaci mafi tsawo tana girki a duniya, a cewar tawagarta.
A watan Janairun da ya wuce ne Failatu Abdul-Razaƙ ta nuna cewa ta kafa sabon tarihi na kwashe sa’oi 227 tana ɗora sanwa.
Ɗaya daga cikin jami’an da ke taimaka wa Failatu, Kafui Dey, a ranar Lahadi a ce yunƙurin nata na kafa tarihi bai yi nasara ba,”ta gaza cimma wasu tsaurarn matakan da kundin ya shimfiɗa.”
“A wata sanarwar da masu lura da kundin suka fitar, ta nuna cewa matar ta karya dokokin wutu, hakan ya sa ta kasa cin nasara.”
Ƴunƙurn kafa tarihin ya jefa ƴanƙasar Ghana cikin farin ciki da annashuwa.
iki har da ƴansiyasa, inda mataimakin shugaban ƙasar, Mahamudu Bawumia da mashahuran mutane da dakarun sojin ƙasar sun bayyana goyon bayansu a gare ta a lokacin da take girkin.
Sai dai duk a rashin nasarar da ta yi, mai dafa abincin ta gode wa magya bayanta.