Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaiwa Ahmadu Haruna Ɗanzago, Shugaban Jam’iyar APC ɓangaren Shekarau ziyarar ta’aziyar rasuwar ɗan uwansa a yau Lahadi a Kano.
Mai taimakawa Ganduje a kan Kafafen Yaɗa Labarai na Zamani, Abubakar Ibrahim ne ya baiyana hakan.
Ya ce Ganduje ya kai ziyarar ne tare da kwamishinonin sa da sauran ƴan siyasa.
PlatinumPost Hausa ta rawaito cewa Ɗanzago shi ne shugaban jam’iyar APC ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau a Kano inda su ke rikici da gwamnan a kan shugabancin jam’iyyar.