fidelitybank

Yanzu mu ka fara luguden wuta a Gaza – Netanyahu

Date:

Isra’ila ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a Gaza waɗanda rahotanni ke cewa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane aƙalla 13.

Sojojin Isra’ila sun ce sun kai harin ne kan abin da su ka kira sansanonin sojojin Hamas.

Hare-haren baya-bayan nan na zuwa ne bayan ruwan wutar da Israi’la ta yi a daren Litinin wanda ma’aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta ta ce ya hallaka mutum fiye da 400.

Isra’ila ta kuma rarraba takardu a wasu sassan Gaza, tana gargaɗin mutane su fice daga yankunan, ciki har da ƙauyen Beit Hanoun.

Isra’ila da Hamas dai sun sami saɓani ne kan yadda za a kai yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar zuwa mataki na gaba bayan mataki na farko ya zo ƙarshe a farkon wannan watan.

A gefe guda kuma Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra’ila za ta cigaba da kai ”hare-hare iya ƙarfinta” kan Hamas a zirin Gaza, inda ya yi gargaɗin cewa za a cigaba da yarjejeniyar ne kawai a cikin luguden wuta, kuma ” yanzu aka fara”

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...
X whatsapp