Tawagar Super Eagles ta ‘yanwasan Najeriya ta kama hanyar komawa gida bayan shafe kusan awa 15 a filin jirgin sama na ƙasar.
Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da hakan a shafinta na X bayan ɗanjarida Adepoju Tobi Samuel ya ce suna shirin shiga jirgin komawa.
Hakan na nufin Najeriya ba za ta buga wasan neman shiga gasar Kofin Afirka ba da aka tsara a gobe Talata da Libya, bayan tashi wasan farko Nigeria 1-0 Libya a makon da ya gabata.