fidelitybank

‘Yansanda sun kashe ‘yan awaren Biafara a jihar Imo

Date:

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta ce gamayyar jami’an tsaron ƙasar ta kashe mambobin ƙungiyar Eastern Security Network (ESN) biyar a jihar Imo da ke kudancin ƙasar.

ESN ɓangaren soji ne na ƙungiyar ‘yan’aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB) da gwamnatin Najeriya ta haramta, wadda ke neman kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin ƙasar.

Mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi, ya faɗa ranar Lahadi cikin wata sanarwa cewa dakarun sun kashe jagororin mayaƙan biyu yayin wani samame a ranar 8 ga watan Fabarairu nan.

Sai kuma a ranar 9 ga watan dakaru suka tare wani rukunin mayaƙan dajin Nkwukwo da ke ƙaramar hukumar Mbaitoli, inda suka sake kashe wasu shugabannin uku yayin musayar wuta, a cewarsa.

Mista Adejobi ya ƙara da cewa jami’ansu sun ƙwace bindiga ƙirar AK-47 bakwai daga hannun ‘yan ƙungiyar, da bindiga harba-ruga 13, da ɗaruruwan harsasai iri-iri.

current eggon news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp