Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta ce ta kama masu aikata laifuka su 2,425 da kuma ceto mutane 55 da akayi ƙoƙarin safararsu, ko garkuwa da su ko kuma sace su a shekarar 2024.
Kwamishina ƴansandan jihar, Salman Dogo Garba ya bayyana hakan yayin da yake ƙarin haske ga manema labarai kan muhimman nasarorin da rundunar ta samu a ƙoƙarinta na yaƙi da laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.
”A farkon shekarar nan, an samu matsalolin tsaro a kananan hukumomi 44 na jihar da suka haɗa da barazanar shigowar ƴanbindiga, garkuwa da mutane da sata a kauyuka da ke ƙananan hukuumomi 17 da ke iyaka da jihohin Kaduna, Katsina, Jigawa da kuma Bauchi.” a cewar shi.
Sai kuma dawowar munanan ayyukan ƴan daba, shaye shaye da kuma wasu muggan laifuka a ƙananan hukumomi takwas da ke birnin Kano, sai kuma rikicin manoma da makiyaya a ƙananan hukumomi 19 da ba sa iyaka kuma ba sa cikin birni.