Rundunar ‘yansanda reshen jihar Ogun, ta tabbatar da kama mutum 21 da ake zargi da shiga ƙungiyar asiri, ciki har da sojojin ƙasar biyu yayin wani samame kan wani otel a birnin Abeokuta.
A cewar kakakin rundunar a Ogun, Omolola Odutola, an kai samamen ne ranar Juma’a bayan samun bayanan sirri game da taron mambobin ƙungiyar Aiye.
Daga cikin abubuwan da suka karɓe daga hannun mutanen akwai bindiga ƙirar gida, da gatari, da shuɗayen huluna masu yawa, da saura kayayyakin da masu asiri ke amfani da su.
“Tuni aka miƙa mutanen ga sashen binciken laifuka da ayyukan asiri domin ci gaba da bincike,” in ji kakakin.