Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il da aka fi sani da Linga ɗan Unguwar Dala, tare da abokinsa Sani Abdulsalam da aka fi sani da Guchi, bisa zargin yada bidiyo suna rike da makamai a TikTok da sauran kafafen sada zumunta.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Laraba, 27 ga watan Agusta, 2025.
A cewar sanarwar, an samu takobi guda ɗaya da sanduna biyu a hannunsu, inda ake zargin suna amfani da bidiyo a shafukan TikTok da Facebook wajen tsoratar da jama’a, abin da ke tada hankulan al’umma.
Kwamishinan ’yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an kaddamar da cikakken bincike kan lamarin, tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana yaɗa bidiyo rike da makamai ko ya shiga harkar ’yan daba, za a gurfanar da shi a kotu.
Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye su ja hankalin yaransu kan guje wa irin waɗannan ayyuka, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.