fidelitybank

‘Yansanda na farautar wadanda suka sace Mata Malaman Coci a Anambra

Date:

Rundunar yansandan jihar Anambra, ta kaddamar da farautar wasu mata biyu malaman coci da aka sace a garin Ufuma da ke karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar.

Cikin wata sanarwar da kakakın rundunar ‘yansandan jihar Tochukwu Ikenga ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne ranar Talata da maraice, lokacin da malaman cocin biyu ke komawa daga wani horon kwarewa da suka halarta a Ogboni.

Kwamishinan yansandan jihar, Nnaghe Oibono Itam, da mataimakinsa sun halarci wurin da lamarin ya faru tare da bayar da umarnin gaggauta nemo inda matan biyu suke, a cewar kakakin yansandan jihar.

Hakan na zuwa ne yan kwanakı bayan wani fitaccen malamin coci a jihar Father Emmanuel Opimma, da aka fi sani da Ebube Murinso, ya yi kira ga gwamnan jihar Anambra, Charres Soludo ya kawo ƙarshen matsalar tsaron da jihar ke tuskanta.

Yayin jawabinsa na sabuwar shekara, Father Obimma, ya bukaci Gwamna Soludo ya sauka daga muƙaminsa idan ba zai ya daƙile masu aikata laifukan da ke ci gaba da yaɗuwa a jihar ba.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp