fidelitybank

‘Yansanda na bincike bayan an tsinci gawar tsohon shugaban Immigiration a Otel

Date:

Rundunar ƴansandan birnin tarayya Abuja ta ce, an samu gawar tsohon shugaban hukumar Shige da Fice ta, David Parradang a cikin ɗakin wani otal.

Cikin wani saƙo da kakakin rundunar ƴansandan birnin, SP Josephine Adeh ta wallafa a shafinta na X, ta ce an samu gawar Parradang mace a wani ɗakin otal da ke yankin Area 3 a Abuja, cikin wani yanayi da yake buƙatar bincike.

Ƴansandan sun ce bayanan da suka samu sun nuna cewa a ranar Talata, 3 ga watan Maris, Parradang ya kama ɗaki a otal ɗin da nufin yin kwana guda inda ya biya naira 22,000.

”Bayan kama ɗakin, wata mace ta ziyarce shi a ɗakin – wadda daga baya ta fice daga ɗakin bayan ƙwace wasu sa’o’i, inda shi kuma aka ame shi a mace bayan haka”, kamar Yadda SP Josephine ta wallafa a shafinta na X.

Ta ƙara da cewa yanzu haka ƴansanda sun faɗaɗa bincike da nufin gano matar domin gano aihinin abin da ya faru har tsohon babban jami’in na shge da fice ya rasa ransa.

punch newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp