Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, ya bukaci rundunar ƴansandan Najeriya ta gaggauta sakin ɗan fafutikar nan Omoleye Sowore ko ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Obi ya bayyana damuwarsa kan matakin da ƴansandan suka ɗauka na ci gaba da tsare Sowore.
”Ina mamakin yadda za a ci gaba da tsare mutumin da ya kai kansa domin amsa gayyatar da ƴansanda suka yi masa”, in ji shi.
Mista Obi ya ce ɗabi’ar da ƴansandan Najeriya ke nunawa ta fara rusa kyakkyawan fatan da ƴan Najeriya ke da shi kan rundunar ƴansandan.
A ranar Laraba ne rundunar ƴansanda Najeriya ta tsare Sowore bayan ya amsa gayyatar da rundunar ta yi masa domin amsa wasu tambayoyi.
Lauyoyinsu sun yi zargin cewa ana ci gaba da tsare shi yanayi na muzgunawa da cin zarafi.
Tuni dai ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama a Najeriya suka fara kiraye-kirayen a sake shi