Al’ummar garuruwan Zurmi da Shinkafi a jihar Zamfara na fuskantar matsin lamba wajen biyan ƴan bindiga kuɗin fansa, da ya kai fiye da naira miliyan ɗari uku.
Yayin da wasu garuruwn kuma ke ci gaba da fuskantar hare-hare tare da kwashe masu kayan abinci, da dabobi.
Hakan dai ya biyo bayan janyewar jami’an sojoji da ke yankin ne, a ranar Litinin da ta gabata.
Bello Hassan Shinkafi shi ne ɗan majalisa mai wakiltar yankin na Zurmi da Shinkafi a majalsiar wakilan Najeriya, ya bayyana hakan a tattaunawarsa da BBC.