Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce ƙasahen yankin Yammacin Afirka ne suka fara rungumar tsarin mulkin dimokraɗiyya hannu bibbiyu a nahiyar Afirka.
Yayin da yake gabatar da jawabi a taron da ƙungiyar shugabannin ƙasashen yankin Yammacin Afirka, Ecowas, shugaba Tinubu ya ce Ecowas na da martaba a idanun duniya saboda yadda take tallafa wa siyasa da zaman lafiya da tsaron yankin.
”Muna buƙatar ƙara nuna kishi ga ci gaban yankinmu, mu samar da yanayin shugabanci mai kyau, da tsarin zirga-zirga mai tsafta tsakanin ƙasashen yankinmu, domin samun ci gaban al’umominmu”, in Shugaban na Najeriya.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa shugaban Laberiya bisa amincewa da shan kaye da ya yi a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin watan da ya gabata.
Ya ce abin da shugaban na Laberiya ya yi wani abin koyi ne da shugabannin ƙasashe za su koyi da shi, yana mai cewa tsohon shugaban Najeriya Good Luck Jonathan ne ya fara yin irin wannan abin a yaba na amincewa da shan kaye a 2015.