fidelitybank

‘Yanbindiga sun sace Kansila da wasu mutune 8 a jihar Kogi

Date:

Wasu rahotanni na cewa ‘yanbindiga sun sace wani sabon kansila da kuma mutum takwas a yankin ƙaramar hukumar Kabba-Bunu da ke jihar Kogi a yankin arewa maso tsakiyar Najeriya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ‘yanbindigar sun kai hari ne a cikin daren da ya gabata da misalin ƙarfe 1:00, inda suka sace mutanen daga gidajensu, ciki har da sabon kansilan da ke wakiltar mazaɓar Odo-Ape Hon. Alaba Ope.

Wani da ya ga yadda lamarin ya faru, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce ‘yanbindigar sun buɗe wuta ne da suka shiga garin da misalin ƙarfe ɗaya na dare, kafin su bi gida-gida su kamo waɗanda suka yi garkuwa da su.

Kusan mako uku baya, aka sace mutum uku da suka haɗa da wani yaro mai shekara takwas a garin.

Jaridar ta ce ta kakakin ‘yansanda na jihar SP William Anya, bai bayar da amsar saƙon da ta aika masa ba na samun bayani game da lamarin, amma ta ce wani babban jami’in tsaro na gwamnati ya tabbatar mata da labarin.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp